OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Rikici ya barke tsakanin Dino Melaye da Samuel Ortom a babban taron jamiyyar PDP

Rikici ya barke tsakanin Dino Melaye da Samuel Ortom a babba

Rikici ya barke tsakanin Dino Melaye da tsohon gwamnan jihar Benue Samuel Ortom a yayin taron shugabannin jam'iyyar PDP na shiyyar Arewa ta tsakiya da ke gudana.

Jigajigan jamiyyar sun yi musayar yawun ne sanadiyar rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar PDP a halin yanzu bayan korar shugaban jam'iyyar na kasa, Damagum. 

A cikin wani faifan bidiyo da aka yada a dandalin X, an ga Dino Melaye yana gargayawa Ortom maganganu marassa dadi.

Dino yace yayi mamakin ganin tsohon gwamnan Benue din a taron bayan ya gama cin dunduniyar jamiyyar.

Bidiyon ya kuma nuna yadda Ortom ya fusata da kalaman Dino Melaye Inda aka ga Ortom yana daga murya yana nuna Dino Melaye da yatsa.

Yayin da rigimar ta ci gaba, sauran jiga-jigan jam’iyyar PDP da mambobin jam’iyyar da suka halarci taron shugabannin sunyi kokarin rabasu Inda suka bukaci Dino da Ortom su kwantar da hankulan su. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci