OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Likitoci masu neman kwarewa a Delta sun kaddamar da yajin aiki

Likitoci masu neman kwarewa a Delta sun kaddamar da yajin ai

Likitoci masu neman kwarewa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Delta, DELSUTH, sun fara yajin aikin gargadi na mako guda kan halin ko in kuka da suka ce gwamnatin Jihar Delta tayi kan al’amuran da suka shafi samar da ingantacciyar kulawar marasa lafiya. 

 

A cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun Dr Harrison Adja Shugaban kungiyar da sakataren kungiyar Dakta Maurice Oghenekaro a ranar Juma'a, 26 ga Afrilu, 2024.

 

 Kungiyar ta bayyana cewa, “Duk da gyare-gyaren da aka yi a baya-bayan nan, kayan aikin har yanzu basa aiki yanda ya dace, Elevator dake jigilar Al'umma bata aikin, duk famfunan Asibitin ya lalace, naurar sanyaya dakin da fankoki duk sun lalace, wannan matsala duk ta gurbata yanayin aiki a asibitin"

Wasu daga cikin tsofaffin naurorin da sanarwar ta ce basa aiki sun hada da "injin CT scan, na'urar duba MRI, injin mammography, injin endoscopy, kayan aikin kasusuwa, na'urar anesthetic, na'urorin motsa jiki, na'urorin duba lafiyar idanu, da na'urar lantarki, da sauransu. 

 

Likitocin sun kuma bayyana cewa rashin isashiyar wutar lantarki da kuma tsadar wutar lantarki da rashin isasshen tallafin kudi daga gwamnatin jihar, yana ci gaba da zama babbar matsala a gare su.

 

Ya kara da cewa, a shirye suke su yi sadaukarwa don samar da ingantacciyar kulawa ga marasa lafiya "Duk da haka, muna kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa da su ja hankalin gwamnatin jihar game da mahimmancin samar da isassun kudaden tafiyar da asibitin wanda shine babbar cibiyar kiwon lafiya a jihar Delta,” in ji sanarwar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci