OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Kyanda ta kashe yara 19 a Adamawa

Kyanda ta kashe yara 19 a Adamawa

Gwamnatin jihar Adamawa ta tabbatar da mutuwar wasu yara 19 da ake zargin sun kamu da cutar kyanda a karamar hukumar Mubi ta Arewa.

 

 Kwamishinan lafiya na jihar, Felix Tangwami ne ya tabbatar da hakan a ranar Asabar ga kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN. 

 

A cewar Tangwami, sama da yara 200 ne aka ruwaito sun kamu da cutar a karamar hukumar, ya ce gwamnatin jihar ta gaggauta samar da likitoci da magunguna ga al’ummar da abin ya shafa bayan samun bayanai kan barkewar cutar a ranar Asabar. 

 

Kwamishinan wanda ya zargi iyaye da kin yi wa ‘ya’yansu rigakafin cutar kyanda a dalilin barkewar cutar, ya tabbatar da cewa za a mika yaran da suka kamu da cutar zuwa asibiti domin kula da lafiyar su.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci