OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Mutane Biyu Sun Mutu Sakamakon Rikicin Filaye a Jihar Neja

Mutane Biyu Sun Mutu Sakamakon Rikicin Filaye a Jihar Neja

Nigerian Police force

Akalla mutane biyu ne suka mutu sakamakon rikicin fili da ya barke tsakanin Fulani da Kambari a garin Salka da ke karamar hukumar Magama a jihar Neja.

A cewar Dangwere Musa, wanda mazaunin garin ne, lamarin ya faru ne a ranar Talata, inda ya ƙara da cewa faɗan da aka yi tsakanin kungiyoyin biyu ya janyo asarar rayuka da dukiyoyi.

“Faɗan tsakanin Kambari da Fulani ya samo asali ne saboda wani fili da bangarorin biyu ke ikirarin nasu ne, a dalilin haka an ƙona ofishin ƴan sanda da gidan hakimin ƙauyen.”

“Hatta Fulani ma an ƙona bukkokinsu sama da 30 a sakamakon haka", cewar Jaridar Punch.

Ya ce rikicin ya faro ne a lokacin da wasu Fulani suka sayi fili a wani yanki yankin Kambaris wanda ba su ji daɗin hakan ba, wanda hakan ya kai ga faɗa.

Ya ci gaba da cewa ƙungiyoyin da ke faɗa da juna sun amince a sasanta rikicin amma sai faɗa ya sake ɓarkewa a tsakanin su, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da asarar dukiyoyi.

“Wannan al’amari ya kasance tun lokacin da wasu Fulani suka sayi fili kuma mutanenmu ba su ji daɗin hakan ba, sai suka yanke shawarar su je su sasanta lamarin.”

“A yayin da ake sasanta rikicin, ɗaya daga cikin Fulanin ya yi amfani da yankansa wajen raunata wuƙansa ya yankk ɗaya daga cikin mutanen da ke gun, daga nan kuma sai fada ya sake tashi."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci