OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Shugaba Tinubu ya ayyana ranar 7 ga watan Afrilu a matsayin ranar yan sanda

Shugaba Tinubu ya ayyana ranar 7 ga watan Afrilu a matsayin

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya ayyana ranar 7 ga watan Afrilu a matsayin ranar ‘yan sanda ta kasa a Najeriya. 

 

Tinubu wanda mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya wakilta ya bayyana hakan a wajen bikin karramawa da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta shirya a Abuja a daren ranar Litinin.

 

 Da yake gabatar da jawabin shugaban kasa mai taken, Kashim Shettima ya ce a yayin da kasar nan ke fuskanta matsanancin yanayin tsaro da yake neman fun karfin jami'an tsaron kasar, alummar Najeriya na iya jurewa su gudanar da alamuran su na yau da kullum cikin nutsuwa sanadiyar jajircewar ‘yan sanda.

 

Ya yi nuni da cewa gwamnatinsa ba zatayi kasa a gwiwwa ba wajen tabbatar da kudurin da ta dauka na sauya akalar rundunar ‘yan sandan Najeriya zuwa yayi daidai da zamani. Hadi da ƙarfafa kwarewa da sanin makamar aiki a tsakanin jamian rundunar.

 

 Shettima ya kuma lissafo wani bangare na sauye-sauyen da gwamnatin tarayya ta yi na sake farfado da aikin ‘yan sanda kamar sanya hannun jari a fannin horar da ‘yan sanda don hakan zai tabbatar da jami’an ‘yan sanda sun samu ilimi da ƙwarewar da ake buƙata don tunkarar ƙalubalen da sukan fuskanta wajen gudanar da aikin su. 

 

Mataimakin shugaban kasan ya tabbatar da cewa gwamnati za ta haɓaka kayan aiki da kimiyya da fasaha don haɓaka ingancin aikin rundunar.

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci