OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Minista Ta Bayar Da Tabbacin Ɗorewar Ayyukan Alheri Na Buhari Bayan 2023

Minista Ta Bayar Da Tabbacin Ɗorewar Ayyukan Alheri Na Buha

Ramatu Tijjani Aliyu

Ƙaramar ministar babban birnin tarayya Abuja, Ramatu Aliyu, ta bada tabbacin cewa ayyukan alheri na gwamnatin shugaba Buhari za su ci gaba da wanzuwa fiye da shekarar 2023.

Ministar ta bayyana haka ne a lokacin da shugaban jam’iyyar APC na ƙasashen waje, Ade Omole ya ziyarce ta a Abuja.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Jcob Ogunseye, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC reshen Burtaniya ya fitar ranar Laraba a Abuja.

Ogunseye ya ce Omole ya ziyarci ministar ne domin ta'aziyyar rasuwar mahaifiyarta, Hajiya Zainab Ali, cewar Jaridar Vanguard.

Ya ce ministar ta gode wa Omole bisa wannan ziyarar, inda ta ce ofishinta zai yi aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumar ƴan ƙasashen waje domin ayyukan gwamnatin nan sun ɗore.

Sa'annan kuma ya yaba mata bisa jagoranci nagari da kuma samar da ingattaccen rayuwa wa al'umma.
 
Gwamnatin Buhari dai ta samar abubuwan more rayuwa ga al'ummar Najeriya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci