Babban taron jam’iyyar APC da ya gudana a Kano a ranar Litinin ya rikide zuwa rikici yayin da sa'insa ya kaure tsakanin shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai Alhassan Doguwa da ɗan takarar mataimakin Gwamnan jihar, Murtala Garo.
Taron wanda aka gudanar a gidan mataimakin gwamnan jihar, kuma ɗan takarar gwamna, Nasir Gawuna, an shirya shi ne domin duba nasarori da gazawar da aka samu a ziyarar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Tinubu ya kai jihar cikin makon nan.
DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa lamarin ya faru ne lokacin da Doguwa, wanda ba a gayyace shi taron ba, ya je ganin shugaban jam’iyyar, Abdullahi Abbas.
Wata majiya ta shaidawa DAILY NIGERIAN cewa, da isar Doguwa wurin taron, ya fara korafin cewa shugabannin jam’iyyar sun mayar da shi saniyar ware kan al’amuran da suka shafi kudi, sai dai a gayyace shi aikin wahala.
“Alhassan Doguwa ya fara afkawa mataimakin gwamnan ne da maganganu kafin da ga bisani ya juya ga Murtala Garo."
Ya yi korafin cewa Murtala ya umurci ‘ya’yansa da su rufe hotonsa a tutocin jam’iyyar yayin ziyarar da Tinubu ya kai masa, alhali Murtala ba shi da masaniya ga me da hakan,” inji wata majiya.
“A wannan yunkuri, Murtala ya yi yunkurin jawo hankalin Doguwa,inda ya tsawatar masa kan rashin da’a, sannan ya tuna masa yadda ya ci zarafin iyayensa a daren da ya gabata yayin wani taro a gidansa a Kwankwasiyya City.”
Bayan haka ne shi Doguwan ya jefi Garo da wani kofi, inda a kokarin karewa ne kuma Garon ya samu rauni a hannun sa.
Majiyar ta shaida cewa daga nan ne Gawuna ya gargadi doguwa da kada ya sake zuwa gidan shi.
0 Tsokaci