Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Kashim Shettima, ya bayyana dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a matsayin dan yawon bude ido a harkar siyasa.
Ya kara da cewa za su yi masa ritaya zuwa kasar Hadaddiyar Daular Larabawa bayan kammala zaben 2023.
Mista Shettima ya bayyana haka ne a wajen gabatar da bikin taron jam’iyyar APC ga ‘yan kasuwa da kuma kamfanoni masu zaman kansu a Legas ranar Talata.
Ya yi wa tsohon mataimakin shugaban kaca kaca inda ya bayyana matsayar karatun sa.
Ya ce takardar shaidar da Atiku ya samu daga Makarantar Kiwon Lafiya ta Kano yace ba wata takarda bace ta azo a gani.
Mista Shettima ya kuma soki Atiku kan dadewa da ya yi yana neman shugaban kasa.
Ya bayyana cewa Atiku ba Abraham Lincoln, tsohon shugaban kasar Amurka bane, Sai dai a kira shi da Raila Odinga ,wanda yayi kaurin suna wajen shan kaye a zaben shugaban kasa a Kenya.
0 Tsokaci