OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 3 Makonni da suka shude

Gwamnatin Tarayya zata samar da cigaba a fannin hakar ma'adanai - Dele Alake

Gwamnatin Tarayya zata samar da cigaba a fannin hakar ma'ada

Dele Alake

Dele Alake, ministan ma’adanan ma’adinai, a ranar Litinin, ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba gwamnatin tarayya za ta samar da wani sabon kamfanin hakar ma’adinai wanda zai bunkasa bangaren a kasar nan.

 

Alake ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a wajen bude taron kwanaki biyu kan ci gaban masana’antar hakar ma’adanai a Najeriya mai taken ‘Duwamammen cigaban Masana’antar Ma’adanai a Najeriya' wanda cibiyar nazarin siyasa da dabaru ta kasa, NIPSS ta shirya, tare da hadin gwiwar Bruit Costaud, a Abuja. 

 

Ministan ya kuma ce tuni gwamnatin shugaba Tinubu ke samun nasarori a fannin ma’adanai, kuma nan ba da dadewa ba shugaban kasa zai samar da gagarumin cigaba a fannin hakar ma’adanai, wanda zai biyo bayan wannan shirin hadin gwiwa da ma’aikatar ma’adanai da gwamnatin Jihar Nasarawa.

 

Alake ya bayyana kwarin guiwar cewa tattalin arzikin dala tiriliyan da shugaban kasa ya yi hasashen za a iya cimma shi kuma zai zarce wannan adadin bisa la’akari da dimbin albarkatun ma’adanai da ma sauran bangarori.

 

 Yace an kafa kamfanonin hakar ma’adanai 150 a matsayin hanyar da za ta magance matsalar hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, da kuma shirin da aka yi kwanan nan kan samar da dakarun dake sanya ido akan ma’adanai ya samar da sakamako mai kyau, inda aka kama masu yiwa fannin zagon kasa da masu daukar nauyinsu.

 

Alake, ya ce dole ne kamfanonin da ke son zuba jari a fannin hakar ma’adinai su samar da hanyar sarrafa shi idan ba haka ba, ba za a ba su lasisi ba, anyi hakan domin dakile yawan fitar da danyen ma'adanan da aka hako a cikin gida zuwa ketare.

 

 Ya ce “Shugaban kasa ya ba mu ikon sake tsara wannan fanni tun daga bincike zuwa samarwa da sarrafa shi da manufar mayar da shi babban mai ba da gudummawa ga tattalin arzikin kasa. 

 

Ministan ya jaddada cewarsa Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabaru ta Kasa, NIPSS ta cancanci yabo don ba da fifiko ga bangaren ma'adinai tare da yaba dabarun da ta dace a cikin tsare-tsaren Shugaba Bola Ahmed Tinubu. 

 

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci