OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Buhari Ya Goyi Bayan Emefiele Akan Sake Fasalin Naira

Buhari Ya Goyi Bayan Emefiele Akan Sake Fasalin Naira

Yayin da ake ta cece-kuce kan matsayin ministar kudi, Zainab Ahmed, kan matakin da babban bankin Najeriya CBN ya dauka na sake fasalin kudin Naira, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana a jiya cewa CBN na da goyon bayansa kan aikin.

 Zainab Ahmed, a karshen makon da ya gabata, ta bayyana cewa CBN ba ta shawarci ma’aikatar ta a cikin sabon tsarin sauya fasalin kudin Naira ba, inda ta yi gargadin cewa sabbin kudaden na iya yin illa ga darajar Naira.

Biyo bayan hakan ne Shugaban babban bankin Godwin Emefele yayi martanin cewar baya bukatar tuntubar ministar kudin domin dokar kasa ta bashi damar chanja fasalin kudi Idan bukatar hakan ta taso.

Hakan ya jefa al'umma cikin rudu, ya Kuma kawo barkewar cece kuce kan wanne daga cikinsu yake kan turbar daidai.

 Sai dai Buhari a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar, ya ce yana da yakinin cewa al’ummar kasar za su samu dimbin nasarori ta yin hakan.

 Da yake magana a wata hira da gidan rediyon Hausa da Halilu Ahmed Getso da Kamaluddeen Sani Shawai, Buhari ya ce, dalilan da CBN suka bayar sun tabbatar masa da cewa tattalin arzikin kasar zai ci moriyar rage hauhawar farashin kayayyaki, jabun kudaden da ake tafkawa a kasuwannin duniya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci