OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Sufeto Janar Na 'Yan Sanda Ya Nada Sabon AIG Na Shiyyar Abuja

Sufeto Janar Na 'Yan Sanda Ya Nada Sabon AIG Na Shiyyar Abuj

IGP Usman Alkali Baba

Babban Sufeto Janar na ‘yan sanda, Usman Baba ya amince da nada Olukayode Egbetokun a matsayin sabon mataimakin sufeto Janar na shiyya 7, dake Abuja.

Egbetokun, wanda ya karbi mukamin mataimakin sufeto Janar na 30 na shiyya ta 7, Abuja a ranar 25 ga watan Oktoba, ya gaji AIG Aliyu Muhammed wanda kwanan nan ya yi ritaya daga aiki.

Egbetokun ya shiga aikin ‘yan sandan Najeriya ne a ranar 3 ga Maris, 1990 a matsayin mataimakin Sufeton ‘yan sanda na Cadet, kwas na 16.

Yayin da ya yi karatun digiri a Jami’ar Legas sannan ya yi digirin digirgir a fannin Injiniya Kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.

Ya rike mukamai masu mahimmanci a cikin rundunar a jihohi daban daban kamar Jihar Osun da Jihar Zamfara da jihar Lagos da jihar Kwara.

Ya kuma halarci kwasa-kwasai da dama a cikin gida da wajen kasar nan.

Egbetokun ya yi alkawarin yin aiki tare da kwamishinonin ‘yan sanda da sauran masu ruwa da tsaki a shiyyar domin inganta ayyukansu.

Ya yi alkawarin ba da kwarin gwiwa wajen tabbatar da manufofin aikin ‘yan sanda na zamani, inda ya ce ba wai kawai a samar da aikin dan sanda mai inganci ba, amma dole ne a samar da dama ga dukkan ‘yan kasa tare da bayar da muhimmanci wajen maido da kuma kara kwarin gwiwa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci