OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 3 Makonni da suka shude

NDE ta kaddamar da shirin horon aikin gona a jihar Oyo

NDE ta kaddamar da shirin horon aikin gona a jihar Oyo

Hukumar da ke kula da ayyukan yi ta kasa NDE a jihar Oyo, ta kaddamar da shirin horar da ci gaban aikin gona mai dorewa na shekarar 2024, SADTS. 

 

Hakan wani bangare ne na sabon yunkurin Gwamnatin Tarayya na sake fasalin fannin noma a kasar nan. 

 

Da yake jawabi a madadin Darakta Janar na NDE, Malam Abubakar Nuhu Fikpo, a wajen bikin kaddamar da shirin horaswar da aka yi a Ibadan, Kodinetan Jihar, Steve-Ogundipe Olayinka, ya ce an yi shirin ne da nufin karfafa gwiwar ‘yan Najeriya marasa aikin yi da su rungumi noma ta yadda za a samar da karin ayyukan yi, tabbatar da wadatar abinci da samar da arziki a kasar.

 

 Darakta Janar din ya kuma mika godiyarsa ga Ministan Kwadago Nkiruka Onyejeocha, wanda ya baiwa hukumar damar bunkasa harkar noma a matsayin sana’ar da za ta iya jawo hankalin ‘yan Najeriya marasa aikin yi zuwa noma na zamani tare da shirin ‘Renewed Hope’ na Shugaba Bola Tinubu. 

 

"A yau, muna nan don ƙaddamar da horon matasa 850, a ƙarƙashin shirin SADTS, wadanda za su halarci taron sun fito ne daga kananan hukumomi na dukkan jihohin kasar nan 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja.”

 

 Ya bayyana cewa horon zai samar da ayyukan yi ga al’ummar karkara ta hanyar fasahar noma ta zamani irin su samar da kayan lambu da dabarun kiwo, tare da inganta rayuwar mutanen karkara, rage ƙaura zuwa birane da nuna wa matasa marasa aikin yi fa'idar noman zamani, da dai sauransu.

 

Hakazali mataimakiyar darakta na sashen samar da aikin yi a karkara, Beatrice Oruoyehu, wacce Chimaobi Eleleme ta wakilta, ta ce an shirya horaswar SADTS ne domin sake fasalin tattalin arziki domin samar da ci gaba mai inganci da kuma bunkasa noma don samun wadatar abinci.

 

Shugaban Sashen inganta ayyukan yi na karkara, a NDE reshen Oyo, Kabir Adedoja, ya bayyana cewa sashen ya fara horon tsahon watanni uku na mutane 50, wadanda aka horar da su a fadin kananan hukumomi uku na jihar. 

 

 Ya shawarci mahalarta taron da su yi amfani da damar da suka samu wajen samun sana’o’in noma da suka dace wanda gwamnatin tarayya za ta samar da su kyauta ta hanyar da ta dace. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci