OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ku zabi wanda zai yi gyara, ku yi watsi da kabilanci -Sanata Bamidele

Ku zabi wanda zai yi gyara, ku yi watsi da kabilanci -Sanata

Sanata mai wakiltan Ekiti ta tsakiya a majalisar wakilai ta kasa, Michael Opeyemi Bamidele, ya bukaci 'yan Najeriya da su zabi Shugaban da zai musu aiki tukuru. 

Yace suyi watsi da ra'ayin banbance-banbancen addini musamman masu sukan zabin APC na Tinubu da Shettima a zaben 2023.

Sanata Bamidele, a wata hira da ya yi da manema labarai a karshen mako a Abuja, ya kuma ce kasar nan na bukatar shugaban da ba ruwan sa da ra’ayin rikicin addini.

Dan majalisar ya ce dimbin kalubalen da kasar ke fuskanta na bukatar wanda yake da ilimin kimiyya da fahimtar matsalolin da kuma hanyoyin da yakamata abi  don magance su.

“A fahimta ta, abin da Najeriya ke bukata a yanzu shi ne shugaban kasa wanda ke da ilimin kimiyya na abin da yakamata a yi, shugaban da yake da fahimtar kimiyyar abin da ba daidai ba, wanda yake da dabarun iya gyara matsalolin al'ummomi, jihohin da sauran su.

“Abinda ya dace shine, muna kuma bukatar wanda zai jajirce  don yanke shawara ba tare da la’akari da ra’ayin wasu tsirari ba.

"Kuma ba tare da ya tashi ya kare wani addini ko kabila ko gungun jama’a ba."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci