OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Jamiyyar APC ta Kano ta dada jaddada kin amincewa da dakatarwar da akayiwa Ganduje

Jamiyyar APC ta Kano ta dada jaddada kin amincewa da dakatar

APC National Chairman, Abdullahi Umar Ganduje

Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta yi watsi da batun dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa Abdullahi Ganduje.

 

Alhaji Zakari Sarina, sakataren jam’iyyar a jihar ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Litinin a Kano.

 

 Ya bayyana dakatarwar da wani bangare na jam’iyyar ya bayyana a ranar Lahadi a matsayin soki burutsu marar tushe yana mai cewa wadanda ke da hannu a cikin dakatarwa ba ‘ya’yan jam’iyyar ba ne. 

 

Sarina ya jaddada cewa, bazai yiwu wadanda BA yan jamiyya bane su dakatar da shugaban jamiyyar na kasa ba tare da bin ka’idojin da kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada ba.

 

"A yayin da muke fuskantar wadannan kalubalen, muna ci gaba da jajircewa wajen ganin mun goyi bayan mai girma shugaban mu na kasa Abdullahi Ganduje,” Sarina ya kammala.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci