OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

NLC ta koka bisa rashin biyan kudaden fansho a jihar Kano

NLC ta koka bisa rashin biyan kudaden fansho a jihar Kano

Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC reshen jihar Kano ta nuna damuwa bisa rashin biyan kudin fansho daya kai kusan naira biliyan 75. 

 

 Shugaban kungiyar NLC reshen jihar Kano, Kabiru Inuwa ya bayyana damuwar kungiyar a lokacin da yake jawabi a wajen bikin ranar ma’aikata ta 2024 da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha.

 

 “Batun rashi biyan kudaden fansho yana da matukar tayar da hankali, inda a halin yanzu bashin fansho da ake bin gwamnati bashi akalla Naira biliyan 75, Wannan yana kawo babbar barazana ga rayuwar yan fansho a jihar" a cewar Inuwa.

 

Kungiyar NLC ta Kano, ta yaba wa gwamnatin Gwamna Abba Yusuf bisa fara biyan cikakken kudin fansho. 

 

Ta bukaci dukkan hukumomin gwamnati da suka gaza fara biyan kudaden fanshon don samun damar biyan kudaden ritaya da hakokin ma'aikatan da suka rasu.

 

Gwamnan jihar, Abba Yusuf wanda mataimakinsa Abdulsalam Gwarzo ya wakilta, ya yi alkawarin gwamnatin jihar na kokarin kyautata rayuwar ma’aikata a jihar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci