OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

Gwamnatin Zamfara zata dauki mataki akan ma'aikatan da suke cin albashi tudu biyu

Gwamnatin Zamfara zata dauki mataki akan ma'aikatan da suke

Gwamna Dauda Lawal na Zamfara ya sha alwashin daukar kwakkwaran mataki kan ma'aikatan da ke karbar albashi fiye da daya a ma'aikatun jihar.

 

A yayin bikin ranar ma’aikata na shekarar 2024 da aka gudanar a Gusau a ranar Laraba, gwamnan ya jaddada bukatar ma’aikata su hada kai da gwamnati wajen tsaftace ayyukan ma’aikatan jihar. 

 

Ya bukace su da su yi watsi da duk wani nau’i na cin hanci da rashawa, inda ya bayyana maaikatan dake karbar albashin tudu biyu suna tallafawa cigaba matsalar.

 

Gwamna Dauda Lawal yace "Nima bana jin dadin karancin albashin ma'aikatan jihar nan Amman kafin mu shawo kan matsalar sai mun fara bincika mun kuma tantance adadin sahihan ma'aikatan jihar"

 

 Gwamnan ya kara da cewar “Don haka ya kamata ma’aikata su ci gaba da hakuri da mu tare da tallafa wa manufofinmu da shirye-shiryenmu don inganta rayuwar ma’aikata,” in ji Gwamnan. 

 

Yana mai tabbatar da cewa da zarar an gama da ma’aikatan bogi, masu karbar albashi da yawa da sauran kura-kurai, za a sanar da sabon mafi karancin albashi. 

 

“Manufofinmu ba wai don mu tozarta kowa ba ne, amma mun kuduri aniyar tabbatar da gyara mai kyau a ma’aikatun gwamnati. Ya zuwa yanzu, mun biya jimillar Naira biliyan 3.841 don biyan kudaden gratuity da fansho ga ma'aikatan jihohi da na kananan hukumomi. Wannan zai ci gaba har sai an biya dukkan kudaden fansho da giratuti gaba daya," in ji shi.

 

 A nasa jawabin shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya NLC reshen jihar Zamfara Sani Haliru, ya yabawa kokarin Lawal na magance matsalolin tsaro da tattalin arzikin da ke addabar kasar.

 

Haliru ya lissafo wasu kalubalen da ke addabar ma’aikata a jihar da suka hada da; jinkirin daga matakin ma'aikatan, rashin aiwatar da mafi ƙarancin albashi.

 

 "Yana da matukar muhimmanci a sanar da gwamna cewa a Zamfara ne kawai ake samun ma'aikata suna karbar kasa da N7,000 a matsayin albashi fiye da shekaru ashirin," in ji shugaban.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci