OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

Kashim Shettima yace gwamnatin tarayya ta kudiri aniyar kawo karshen cin hanji da rashawa

Kashim Shettima yace gwamnatin tarayya ta kudiri aniyar kawo

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta kuduri aniyar kawo karshen cin hanci da rashawa ba tare da tsoro ko son rai ba.

Shettima ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a taron Chronicle Roundtable a Abuja, inda ya ce gwamnati na kokarin ganin ta rage yawan marasa aikin yi a kasar. 

Taron ya mayar da hankali ne kan nazarin yadda tsarin tafiyar da tattalin arziki da zamantakewar gwamnatin Tinubu zai sauya Najeriya.

Cikin wadanda suka halarci taron sun hada da ministan yada labarai, Mohammed Idris; Mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin siyasa a ofishin mataimakin shugaban kasa Hakeem Baba-Ahmed; da tsohon ministan kudi, kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Shamsudeen Usman; da sauransu.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, na tuhumar wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulki, bisa zargin cin hanci da rashawa, kamar tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, bisa tuhume -tuhume 19 da suka hada da halartar kudin haram da cin amana, da karkatar da kudade har Naira biliyan 80.2. 

Yahya Bello ya kasance gwamnan jihar Kogi daga ranar 27 ga watan Junairu, 2016, zuwa 27 ga watan Janairu, 2024.

A ranar 17 ga Afrilu, 2024, jami’an EFCC sun yi wa Yahya Bello kawanya a Abuja don kama shi amma ana zargin Gwamna Ododo ya tallafa wajen fitar da shi daga gidan. 

A wannan lokacin hukumar EFCC ta yi gargadin cewa ba za ta amince a kawo cikas ga ayyukanta ba, matakin da babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi ya goyawa baya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci