OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

Hukumar Alhazai NAHCON ta sanar da ranar fara jigilar alhazai a hajjin bana

Hukumar Alhazai NAHCON ta sanar da ranar fara jigilar alhaza

Hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta sanar da cewa jirgin farko na maniyata zai tashi a ranar 15 ga watan Mayu domin fara aikin hajjin bana.

Shugaban Hukumar NAHCON, Malam Jalal Ahmad Arabi ne ya bayyana haka a jawabinsa na bude taron masu ruwa da tsaki akan aikin Hajji da Umrah na bana da aka gudanar a cibiyar Shehu Musa Yar’adua da ke Abuja. 

Arabi ya sanar da cewa, kusan mahajjatan Najeriya 65,500 ne za su halarci aikin Hajjin shekarar 2024, inda ya kara da cewa kamfanonin jiragen sama da aka amince da su za suyi jigilar alhazai daga cibiyoyi 10 na tashi da saukar jiragen sama na kasar.

Shugaban hukumar alhazai ta kara da cewa a wannan karon daukacin alhazan Nageriya zasu samu damar yin kwanaki hudu a Madina kafin a fara gudanar da aikin hajjin bana.

Arabi ya ce hukumar alhazan ta ga ya dace ta tattauna da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da an gudanar da aikin Hajji cikin nasara a bana.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci