OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Gwamnatin Tarayya zata fara rushed gidajen dake kan hanyar Legas zuwa Calabar

Gwamnatin Tarayya zata fara rushed gidajen dake kan hanyar L

Abuja-Kaduna highway aerial view

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za a fara rusa gine-ginen da ke kan kilomita ukun farko na babbar hanyar Legas zuwa Calabar a ranar Asabar 27 ga watan Afrilu. 

 

Kwanturolan ayyuka na gwamnatin tarayya a Legas, Keisha Korede, ita ce ta bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Legas ranar Alhamis. 

 

Ta bayyana cewa rusau din zai shafi duka gine-ginen ke kan kilomita ukun farkon titin. Korede ta ƙarfafawa mamallakan kadarorin da suka karɓi sanarwar rusau kuma suke da wata damuwa su ziyarci sakatariyar ma'aikatar ayyuka ta tarayya daga ranar Alhamis, 25 ga Afrilu, har zuwa Juma'a, 26 ga Afrilu don magance damuwarsu. Ta ce, "Bayan haka, tawagar rusau din za ta fara aiki da safiyar ranar Asabar na tsawon kilomita uku na farko kuma zasu rushed duk wani gini da ke kan babbar hanyar Legas zuwa Calabar" 

 

 “Don haka, ina so in yi amfani da wannan kafar wajen sanar da masu kadarorin za a warware matsalolinsu tsakanin yau da gobe."

 

 Aikin babbar hanyar Legas zuwa Calabar mai tsawon kilomita 700 an yi shi ne domin ya hada Legas zuwa Cross River, ya ratsa jihohin da ke gabar tekun Ogun, Ondo, Delta, Bayelsa, Rivers. da Akwa Ibom, kafin ya isa Cross River. 

 

Za a kashe Naira triliyan 15 wajen gina hanyar bakin teku mai tsawon kilomita 700 daga Legas zuwa Calabar kuma kowane kilomita zai ci Naira biliyan hudu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci