OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 4 Makonni da suka shude

Jamiyyar APC ta dage zaben fidda gwanni a mazabu 13 a jihar Ondo

Jamiyyar APC ta dage zaben fidda gwanni a mazabu 13 a jihar

Sakamakon isar kayan aiki da ma’aikata a makare zuwa mazabu 13 a karamar hukumar Okitipupa ta jihar Ondo, kwamitin zaben fidda gwani na jam’iyyar APC ya dage gudanar da zaben fidda gwannin kujerar gwamna zuwa ranar Lahadi 21 ga Afrilu, 2024. 

 

Wata sanarwa da shugaban kwamitin zaben Alhaji Ahmed Ododo ya fitar a Akure, ta ce an dage gudanar da zaben fidda gwani na karamar hukumar ne biyo bayan rashin zuwan ma'aikata da kayan aiki akan lokaci.

An gudanar da zaben fidda gwani na gwamna a fadin mazabun 203 na jihar a ranar Asabar 20 ga watan Afrilu.

 

 ‘Yan takarar gwamna 16 ne suka fito zaben wanda kwamitin gudanarwa mai mutane bakwai suka gudanar karkashin jagorancin gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo.

 

 A cewar Ododo, “Bayan samun rahoton zaben fidda gwani na mazabu 203 da ke kananan hukumomi 18 na jihar Ondo, kwamitin zaben fidda gwani ya yanke shawarar cewa za a gudanar da zaben a dukkan Unguwani 13 na karamar hukumar Okitipupa tare da wadanda suka yi rijista 9,515.

 

 Ya bayyana cewa, hakan ya faru ne saboda ingantattun rahotannin da ke nuna cewa zaben bai gudana a karamar hukumar ba saboda jinkirin isar kayan aiki da ma’aikata.

 

Yace "Za a gudanar da zabe a karamar hukumar Okitipupa da karfe 12 na rana ranar Lahadi 21 ga Afrilu, 2024.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci