OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

Gwamnatin Tarayya ta bada tabbacin matsalar man fetur na dab da zuwa karshe

Gwamnatin Tarayya ta bada tabbacin matsalar man fetur na dab

Gwamnatin tarayya ta bada tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za'a kawar da matsalar karancin man fetur a fadin kasar. 

Ko’odinetan shiyyar Kudu maso Yamma na NMDPRA, Engr. Ayo Cardoso ya bayyana hakan a wata sanarwa. 

Duk da cewa kamfanin man fetur na NNPCL ya ba da tabbacin cewa yana da isasshen man da zai ishi bukatar kasar, amma ana ci gaba da samun karancin man. 

Cardoso ya ce kwanaki biyu da suka wuce kasar ta samu lita 300 na man fetur din haka babu bukatar alumma su firgita domin dogon layin man fetur yazo karshe. 

"Kamar yadda na fada a baya, za a samu isasshen mai a fadin Najeriya nan ba da dadewa ba. Mun samu sama da lita miliyan 300 a ranar Talata. An karo wasu motocin man fetur din ma amman ban san alkaliman ba tukun kuma za'a cigaba da kawo motocin mai har tsawon na kwanaki 15 daga ranar Litinin."

Cardosa ya tabbatar da cewa zasu rarraba man ga jihohi ba tare da nuna babbanci ko nuna fifiko.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci