OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Dole Ne Arewa Ta Magance Matsalar Tsaro Don Samun Cigaba - Goje

Dole Ne Arewa Ta Magance Matsalar Tsaro Don Samun Cigaba - G

Senator Danjuma Goje

Sanata Danjuma Goje mai wakiltar mazabar Gombe ta tsakiya ya bayyana cewa Arewa ba za ta kai ga cimma burinta ba har sai ta magance matsalar tsaro a yankin.

Tsohon gwamnan jihar Gombe ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wani littafi mai taken ‘Rashin Tsaro da Tattalin Arzikin Arewacin Najeriya a Karni na 21: wanda aka gudanar a dakin taro na Shehu Musa Yar’ Adua dake Abuja.

Littafin wanda aka rubuta kuma aka hada shi don karrama Shugaban Majalisar Gudanarwa na Jami’ar Abuja, Farfesa Ahmed Madibbo, wanda Farfesa Maiyaki Mejida na Jami’ar Jihar Nasarawa ya shirya shi.

Goje ya yi nuni da cewa, tun da farko matsalar rashin tsaro ta bangaren ‘yan fashi, garkuwa da mutane da ta’addanci sun faro ne da rikicin Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas.

Wanda yanzu ya faɗaɗa ya mamaye Arewacin Najeriya, har ma da kusan ɗaukacin ƙasar baki ɗaya.

“Arewa ba za ta taɓa samun ƙafafunta ba, ba tare da magance matsalar tsaro ba, cewar Jaridar Punch.  

"Duk kukan da ake yi na dimokuradiyya da ci gaban ƙasa ba za a iya cimma su ba a cikin wani yanayi na rashin tsaro na gama-gari kamar yadda ake samu a kusan dukkan lungu da sako na Arewacin Najeriya.

"Wannan littafi tabbas zai taimaka sosai wajen daƙile matsalar rashin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziƙi a arewacin Najeriya."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci