OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gwamnan Gombe Ya Nada Alkali Sabon Shugaban Hukumar Tattara Kudaden Shiga

Gwamnan Gombe Ya Nada Alkali Sabon Shugaban Hukumar Tattara

The New Chairman of the Gombe State Board of Internal Revenue Service, Salihu Baba Alkali|

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya amince da nadin Salihu Baba Alkali a matsayin shugaban hukumar tattara kudaden shiga na jihar Gombe.

Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ne ya bayyana hakan.

Njodi ya ce nadin ya fara aiki nan take.

Kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Ismaila Uba Misilli ya fitar, Alkali ya taba rike wannan matsayin na hukumar kudaden shiga.

Sabon shugaban hukumar kudaden shigan dai tsohon darakta ne mai ritaya a hukumar tara haraji ta tarayya (FIRS) kuma kwararre kan harkokin kudi da haraji.

Alkali yana da rajista da kungiyar kwararrun masu tattara haraji na Najeriya, kwararrun akantoci na tarayya da kuma Nigerian Institute of Management.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci