OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

ACF Za Ta Bada Tallafin Karatu Ga ƴan Asalin Kano

ACF Za Ta Bada Tallafin Karatu Ga ƴan Asalin Kano

Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) reshen jihar Kano ta yi alkawarin samar da shirin bayar da tallafin karatu ga ‘yan asalin jihar da ba za su iya biyan kudin karatun manyan makarantu ba.

 Sabon zababben shugaban kungiyar Dakta Umar Faruk Gwani ne ya bayyana hakan a Kano a jawabinsa na karramawa, inda ya ce matakin ya zama dole domin a halin yanzu gwamnati ta mika harkar ilimi ga yan kasuwa.

 Jaridar daily trust ta ruwaito cewa an zabi sabbin shugabannin kungiyar ta ACF ba tare da hamayya ba a babban taronta na shekara-shekara (AGM) da aka gudanar a Kano.

Sabon shugaban ya kuma sha alwashin ba da fifiko kan harkokin tsaro ta hanyar bin diddigin al’umma don tallafa wa hukumomin tsaro da kungiyoyin sa kai a yakin da ake da muggan ayyuka.

 Sabon shugaban ya kara da cewa taron zai kuma jawo hankalin ‘yan takarar gwamna na jam’iyyu daban-daban kan tsarinsa, musamman a fannin ilimi, kiwon lafiya, tsaro, noma da karfafa matasa da mata.

 A lokacin da yake kaddamar da sabbin shugabannin kungiyar ACF shugaban kwamitin amintattu na Kano, Janar Halliru Akilu (Rtd) ya bukace su da su tabbatar da amincewar da aka yi musu.

 Janar Akilu ya dora wa sabbin shuwagabannin aikin samar da tsare-tsare da manufofin da za su kai Kano da Arewacin Najeriya gaba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci