OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ƴan Bindiga Sun Ƙona Shaguna Da Motoci A Anambra

Ƴan Bindiga Sun Ƙona Shaguna Da Motoci A Anambra

Ƴan bindiga sun ƙona shagona 15 da manyan motoci da kuma ƙanana a unguwar Amarka da ke ƙaramar hukumar Ihiala a jihar Anambra.

A cewar wani ganau, harin ya faru ne ran Alhamis da dare, yayin da ƴan bindigan, waɗanda yawansu ya haura 10, sun  yita harbe-harba cikin dare.

Ya ƙara da cewa anyi awon gaba kayayyaki a cikin shagunan a yankin.

“harbin ya haifar da tashin hankali yayin da mazauna garin da matafiya suka bar shagunansu da ababen hawan su domin tsira da rayukansu.

Harbin ya haifar da cunkoson ababen hawa wanda ya taso daga Amorka zuwa Mgbidi da Awo-omma a jihar Imo.

“A cikin ruɗani, ƴan bindiga sun yi awon gaba da kaya masu tarin yawa a shaguna da dama.

“Wasu mutane sun ce ƴan kungiyar IPOB ne da ke zanga-zangar cewa ba a saki shugabansu, Nnamdi Kanu ba, duk da umarnin kotu,” inji wata majiya.

Wata majiyar kuma ta yi ikirarin cewa ƴan ta’addan sun kuma jefar da takarda, dauke da sakwannin rubutu, suna masu cewa ba za a samu zaman lafiya ba har sai an sako Kanu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci