OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

ASUU: A Yau Laraba Ne Ake Sa Ran Rassan ASUU Zasu Kaɗa Ƙuri’a

ASUU: A Yau Laraba Ne Ake Sa Ran Rassan ASUU Zasu Kaɗa Ƙur

ASUU

A cigaba da yajin aiki da ƙungiyar ASUU keyi, a yau Talata da kuma gobe Laraba ne za a fara kaɗa ƙuri’a na reshen ƙungiyar malaman jami’o’i.

Za a miƙa hukunce-hukuncen rassa daban-daban ga majalisar zartarwa ta ƙasa domin yanke hukunci na ƙarshe.

Wata Majiya mai tushe ta bayyana hakan a wata tattaunawa da ta yi da wakilin Jaridar Punch a Abuja ranar Talata.

“Mun samu umarnin bayan ganawar da shugaban majalisar a jiya (Litinin).  

"Shiga tsakanin yayi daidai a wannan lokaci kuma ya dace, Sassan za su kaɗa ƙuri’a daga yau zuwa gobe daga nan ne za a gabatar da shawarar ga kwamitin zartaswa,” inji majiyar.

Rahoton yace sabon lamarin ya zo ne bayan ganawar da shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, wanda ya ƙira tarurruka da dama tsakanin kungiyar da bangaren gwamnatin tarayya.

Babban lauyan kungiyar ASUU, Femi Gbajabiamila ya bayyanna cewa za a kawo ƙarshen yajin aikin nan da ƴan kwanaki.

A ranar Litinin, 14 ga Fabrairu, 2022 ASUU ta shiga yajin aikin saboda abin da ƙungiyar ta bayyana a matsayin gazawar gwamnati wajen biyan buƙatun ƙungiyar.

Ministan kwadago da samar da ayyuka, Chris Ngige ne ya maka malaman da suke yajin aiki zuwa kotun masana'antu ta ƙasa.

Yayin da a ranar 21 ga watan Satumba ne kotun masana’antu ta ƙasa ta umarci ASUU da ta janye yajin aikin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci