OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

Shugaba Tinubu yayi ta'aziyyar mutuwar Sidi Ali

Shugaba Tinubu yayi ta'aziyyar mutuwar Sidi Ali

Shugaban kasa Bola Tinubu ya jajanta wa iyalai da abokan huldar tsohon dan majalisar dokoki a jamhuriya ta biyu kuma fitaccen dan jarida, Sidi Ali. 

 

Sanarwar ta fito ne daga bakin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale a ranar Laraba a Abuja. 

 

Sidi Ali, wanda babban jigo ne a jam’iyyar APC, kuma tsohon dan majalisar wakilai, ya rasu ne a ranar 25 ga watan Afrilu. 

 

Marigayin ya kasance kwararren marubuci, inda ya wallafa littattafai 19 da kasidu da dama.

 

 “Wasu daga cikin fitattun ayyukansa sun haɗa da, ‘Tafiya zuwa Timbuktu’ (1965); ‘Corruption in High Society’, and ‘The Power of Power on Muhammad Ribadu, former Minister of Defence’ (1982).

 

Da yake karin haske kan gudunmawar da marigayin ya bayar a kasar, Tinubu ya ce rawar da ya taka a matsayinsa na dan jarida ya taimaka wa Najeriya a lokacin da kasar ke tsananin bukatar taimakon sa.

 

 Shugaban ya yi addu’ar Allah (S W.T) ya jikan marigayin ya kuma jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Kano bisa wannan rashi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci