OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Jami'ar Ahmadu Bello ta sanar da ranar da za ta dawo bakin aiki

Jami'ar Ahmadu Bello ta sanar da ranar da za ta dawo bakin a

Hukumar gudanarwar Jamiar Ahmadu Bello da ke Zaria, ta fitar da sanarwar cewa ranar Litinin 24 ga watan Oktoba za ta dawo bakin aiki.

 

Sanarwar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami'ar ta fitar a yau Laraba.

 

Sanarwar ta ce an tsaidai ranar ne bayan taron gaggawa na majalisar jamiar da ta gabatar karo na 516.

 

 

Jamiar Ahmadu Bello Zariya za ta bude makaranta a ranar Litinin 24 ga Oktoba 24, 2022 domin ci gaba da karatu bayan amincewa da sabunta kalandar karatu na shekarar 2021/2022 da Majalisar jami'ar Jamiar ta yi a taronta na 516 a yau Laraba, 19 ga watan Oktoba 2022.

 

Kalandar, wanda majalisar zartarwa na jami'ar ta amince da shi a taronta na yau da kullun karo na 513 wanda aka gudanar tun a ranar 25 ga Nuwamba, 2021 jami'ar tace ya zama dole a sake sabunta kalandar saboda yajin aikin ASUU da aka shafe watanni takwas ana yi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci