OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Hukumar JAMB Ba Ta Soke Damar Shiga Makarantu Ba – Magatakarda

Hukumar JAMB Ba Ta Soke Damar Shiga Makarantu Ba – Magatak

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB a jiya ta ce ba ta soke ko dakatar da duk wani shiga jami’o’i ko kwalejin fasaha ko kwalejojin ilimi ba, sakamakon yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’in, ASUU ta yi.

 Babban magatakardar hukumar ta JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ne ya bayyana haka kafin ya ayyana bude taron majalisar zartarwa ta kasa, NEC, na kungiyar masu zaman kansu na ilimi NASU, a Abuja.

 Farfesa Oloyede ya ce: "Tsarin shigar da dalibai ya ta'allaka ne akan cibiyoyi daban-daban. JAMB cibiyar sadarwa ce Bata da hurumin Yankee hukunci akan zagayen Karatun jami'o'i. Kuna sane cewa jami'o'i da cibiyoyi na musamman har yanzu suna cikin zaman karatun su na 2020/2021. Wasu suna cikin zaman karatun 2021/2022 wasu kuma suna cikin zaman karatun 2022/2023.Shawarata ita ce, ya kamata dalibayai su tuntubi cibiyoyinsu domin sanin wane zaman da ake yi kuma su tuntubi JAMB domin neman karin haske"

Farfesan ya kara da cewa "Ba a soke izinin shiga kowane zangon Karatu ba, ko na wata cibiya. Dukkanmu muna da jarabawar shiga wannan zama guda uku kuma ba su kubuce ba yanzu ya kamata hukumomi su tantance matakin da za a dauka nan gaba.”

 A halin da ake ciki, dan rajin kare hakkin dan Adam, kuma babban Lauyan Najeriya, SAN, Mista Femi Falana, ya roki Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, da sauran wadanda suka bukaci ASUU ta dakatar da yajin aikin da su roki Gwamnati ta cika nauyin da ya rataya a wuyanta ga kungiyar da biyan mambobi albashinsu.

 Falana wanda shi ne lauyan ASUU, ya bukaci hakan ne a jiya a yayin da yake gabatar da lakca yayin taron Masu ruwa da tsaki Jami’ar Augustine, dake Ilara Epe, Legas.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci