OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

NLC da TUC sun bukaci gwamnatin tarayya tayi gaggawar dakatar da karin kudin wutar lantarki

NLC da TUC sun bukaci gwamnatin tarayya tayi gaggawar dakata

Shugabanin kungiyoyin kwadagon NLC da TUC Joe Ajaero fa Festus Osifo sun bukaci gwamnatin tarayya ta jayne batun karin kudin wutar lantarki da tsarin raba adadin wutar da kowanne tsagin alumma zai samu.

 

Sunyi wannan kira yayin bikin ranar ma'aikata da aka gudanar 1 ga watan Mayu a Abuja.

 

Shugabanin kungiyoyin kwadagon sun gabatar da jerin bukatu 18 ciki harda batun dakatar da karin kudin wutar.

 

Sun kuma bukaci gwamnatin ta gaggauta samar da motoci masu amfani da gas kamar yadda tai alkawari tun da fari.

 

Yan kwadagon sun gabatar da bukatar dakatar da karbar haraji na tsawon shekara daya a hannun masu kananan sanaoi.

 

Hukumar kula da wutar lantarki NERC ta sanar da karin kudin wutar a ranar 3 ga watan Afrilun daya gabata, Wanda sukace ya shafi wadanda suke rukunin band A dake samun wutar tsawon awannin 20 a rana.

 

Yanzu alumma zasu dinga biyan N225 akan kowane Kilowatt maimakon N66 dayake a baya, hakan ya jawo tofun Allah tsine a wajen Yan Najeriya musamman la'akari da tsananin tattalin arzikin da ake fama da shi.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci