OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

ASUU: Ɗalibin Koyon Aikin Jinyan Da Ya Koma Saida Abinci Ya Rasu

ASUU: Ɗalibin Koyon Aikin Jinyan Da Ya Koma Saida Abinci Ya

Late Usman Abubakar Rimi

Ɗalibin da ke karatun likitanci da tiyata na Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto (UDUS), Usman Abubakar-Rimi wanda ya tsunduma harkar sayar da abinci ya rasu.

In zaku iya tunawa mun ruwaito cewa Abubakar-Rimi ya buɗe wata cibiyar samar da abinci da taliyar a Unguwar Diflomasiyya da ke Sakkwato.

Rahoto daga kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN ya ce ɗalibin ya rasu ne a ranar Laraba bayan gajeriyar jinya.

Da yake tabbatar da rasuwar a ranar Asabar din da ta gabata, Umar Idris, wanda ya kasance na kusa da marigayin ya ce tuni aka binne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Rahoton yace an binne marigayin a mahaifarsa Rimi, dake cikin ƙaramar hukumar Rimi ta jihar Katsina.

Ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai tawali’u kuma ɗalibi mai kwazo kuma hamshaƙin ɗan kasuwa.

A cewarsa, marigayin ya kasance ko’odinetan cibiyar ‘yan kasuwa na karni na 21 na jihar Katsina, kuma ya taka rawar gani wajen daidaita harkokin kasuwanci a duniya a shekarar 2019 da 2020.

Ya ƙara da cewa marigayin ya ya riƙe muƙai da dama wanda yayi amfani dasu wajen inganta rayuwar mata da matasa masu sha'awan dogaro da kansu.

Har ila yau, Marigayi Abubakar ya jagoranci matasa da yawa don fahimtar dasu amfani da lokacin su yadda ya kamata, musamman a lokacin kulle na Corona da yajin aikin watanni 8 na ASUU.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci