OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

Ranar ma'aikata: Gwamnatin Kano zata samar da gidajen ma'aikata a farashi mai sauki

Ranar ma'aikata: Gwamnatin Kano zata samar da gidajen ma'aik

Governor Abba Kabir Yusuf

Gwamnan jihar Kano Abba Yusuf ya tabbatar da aniyarsa na inganta walwala da jin dadin ma'aikatan jihar. 

 

Ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatin sa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an biya ma’aikatan dalbashi a kan lokaci da kuma kudaden fanshon wadanda sukayi ritaya domin inganta rayuwarsu. 

 

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin bikin ranar ma’aikata ta duniya da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.

 

Gwamnan wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo ya wakilta ya bayyana cewa an fara shirye-shiryen samar da gidaje ma’aikata.

 

 A cewarsa, da zarar an kaddamar, zai baiwa ma’aikata damar siyan gidaje a farashi mai sauki.

 

Ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa ta ba da fifiko wajen bunkasa ilimi, noma da kiwon lafiya da dai sauransu. 

 

Gwamna Yusuf ya yi kira ga ma’aikatan da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu.

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci