OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

APC Ba Za Ta Ci Zaɓen 2023 Ba Idan Ba Gwamnoni, Cewar Abdullahi Adamu

APC Ba Za Ta Ci Zaɓen 2023 Ba Idan Ba Gwamnoni, Cewar Abdul

Shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu ya ce jam’iyyar za ta sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa a 2023 ba tare da goyon bayan gwamnonin jam’iyyar ba.

Shugaban ya bayyana haka ne a wajen taron gwamnoni da kwamitin gudanarwa na jam'iyar da masu ruwa da tsaki a Abuja.

A taron wanda ya gudana a ranar Laraba, Adamu ya ce, “Kasancewar su manyan jami’an gudanarwa na jihohinsu daban-daban, aikin babbar jam’iyyarmu yana hannun Allah kuma a hannunsu domin su ne kwamandojin yaƙin jam’iyyar a jihohinsu daban-daban.

“Ba za mu iya samun ci gaba mai ma’ana a al’amuran jihohin nan ba, musamman a shekarar zabe da ke gabatowa. 

"Ba za mu iya yin shiri ba tare da neman gudumawan gwamnonin mu ba domin mu tsaya tare, mun yarda cewa muradin mu daya ne.

“Za mu yi shiri tare don ganin yadda za mu iya isar da muradun jam’iyyar tare da tabbatar da cewa nasara ta zama tamu a babban zaben 2023.

A nashi jawabin, babban daraktan kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa jihar Filato, Simon Lalong, ya ce Adamu ya kira taron ne domin tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban jam’iyyar.

Daga ƙarshe ya nemi goyon ƴaƴan jam'iyar a kowane mataki don ganin an samu nasara a zaɓen da ke tafe, cewar Jaridar Daily Trust.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci