OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Jam'iyyar ADC Ta Dakatar Da Shugabanta A Kogi

Jam'iyyar ADC Ta Dakatar Da Shugabanta A Kogi

Jam’iyyar ADC reshen jihar Kogi ta dakatar da shugaban jam’iyyar na jihar, Kingsley Temitope Oggah bisa zargin almubazzaranci da kudade da kuma wasu manyan laifuka.

Mataimakin shugaban jam'iyyar na jihar Momoh Jimoh Sule Gomina ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Litinin bayan taron majalisar zartarwar jihar a Lokoja.

A cewar Gomina, matakin ya biyo bayan kada kuri’ar rashin amincewa da shugaban karamar hukumarsa ne a ranar 25 ga watan Agusta, 2022, yayin da wakilai 13 daga cikin 15 na jam’iyyar reshen jihar Kogi suka rattaba hannu kan dakatarwar.

Shugaban gundumar ya aika da wasikar dakatarwa zuwa ga majalisar zartarwa na karamar hukumar da na jihar a ranar 9 ga Satumba, 2022.

Hukumar zartaswar jihar bayan taron ta a ranar Litinin ta gyara dakatarwar tare da umurtan sakataren, Adaji John da ya karbi ragamar tafiyar da harkokin jam’iyyar na rikon kwarya.

“Sakamakon haka, mambobin kwamitin zartaswa na jihar sun amince da kudurin rashin amincewa da shi da kuma dokar dakatarwa daga sassan jam’iyyar a jihar.

“Dakatar da Kingsley Temitope Oggah ya faru ne saboda wasu ayyuka na adawa da jam’iyya, da rashin da’a, kalaman da ba su daceba da nufin bata sunan jam’iyyar.

"Sa'annan yunkurin dagula babbar jam’iyyar mu ta hanyar yada rashin adalci da ya saba wa doka ta 6, sashe na 1, 2.  kuma 4;  Mataki na 22 sashe na 6 da kuma sashi na 32 wanda ya shafi rantsuwar aiki.

Sanarwar ta kara da cewa, “An umurci sakataren jihar, Comrade Adaji John da ya karbe dukkan kadarorin jam’iyyar da ke hannun dakataccen shugaban jam’iyyar, tare da jagorantar al’amuran jam’iyyar na wucin gadi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci