OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Kwankwaso Zai Doke Atiku, Da Tinubu A Zaben 2023: Jigon Jam’iyyar NNPP

Kwankwaso Zai Doke Atiku, Da Tinubu A Zaben 2023: Jigon Jam�

2023 Presidency: Many APC Lawmakers are joining Senator Rabi'u Musa Kwankwaso in the NNPP

Wani jigo a jam’iyyar NNPP, Alhaji Ahmed Tijjani, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Sanata, Rabi’u Kwankwaso zai doke sauran ‘yan takara wajen lashe zaben 2023.

Tijjani ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Kamfanin dillancin Labarai na Kasa NAN a ranar Lahadin nan a Kaduna.

Inda ya ce "Idan ka lura da yanda jam'iyyar ta samu karbuwar a wajen talakawan Najeriya za ka yarda da ni cewa babu abin da zai hana mu ci zaben 2023"

“Kalli irin gagarumin tarbar da ake yi wa jagoranmu Sanata Rabi’u Kwankwaso a duk lokacin da ya ziyarci wani gari ko wata jiha, za ka ga dimbin jama’a da suka fito domin tarbarsa, tun kafin yakin neman zabe.

Tijjani ya ce ba kamar sauran ‘yan takarar shugaban kasa ba, Kwankwaso yana da nasarori da dama da ya nuna a mukaman sa na shugabancin kasar nan a baya.

“Ku dubi manyan ‘yan takarar shugaban kasa guda hudu a 2023 misali, Bola Tinubu zai ce muku ku zabe Ni, Ni kuma zan yi wannan da wancan, Atiku Abubakar ma zai fadi haka. Peter Obi ya bayyana a matsayin dan takarar shugaban kasa ne kawai a shafukan sada zumunta.

“Amma NNPP tana gaya wa mutane cewa Kwankwaso ya yi haka kuma a jihar Kano da sauran jihohin tarayya, idan ya samu wa’adin mulki a 2023 zai kwaikwayi abin da ya yi a baya, har ma ya kara.

“Ba wai kawai yana zuwa ne ya yi alkawura kamar sauran ba, abin da muke cewa shi ne Kwankwaso ya taba yi, zai sake yi idan ya samu dama,” inji shi.

Tijjani ya ce PDP da APC sun gazawa ‘yan Najeriya ta kowacce fuska, don haka akwai bukatar sabuwar jam’iyyar da za ta karbi ragamar shugabancin kasar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci