OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Matasa Uku Sun Tsere Daga Wadanda Suka Yi Garkuwa Da Su A Abuja

Matasa Uku Sun Tsere Daga Wadanda Suka Yi Garkuwa Da Su A Ab

Rahotanni sunce wasu matasan Fulani guda uku da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a Gwanda, a unguwar Gurdi da ke unguwar Abaji a Abuja sun kuɓuta.

Rahoton da Daily Trust ya ce matasan sun tsere ne bayan da masu garkuwa da su suka yi barci.

A martanin sa, Kansila mai wakiltar Gurdi Ward, Wozhe Ishaya, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis.

Ya ce ƴan bindigar sun kai farmaki matsugunin Fulani a yankin da misalin karfe 11 na daren ranar Talata inda suka yi awon gaba da yaran wanda shekarunsu ya kama daga 12 zuwa 16 .

“Amma cikin ikon Allah, ƴan bindigar sun yi barci, ba su ɗaure su ba, a lokacin yaran suka tsere,” in ji shi.

Ya ce ƴan fashin sun kuma kwashe wasu dabbobi zuwa maɓoyar tasu, suka yanka su.

A martanin Hakimin Gulida, Abubakar Sadauna, ya yi Allah wadai da harin da ƴan bindiga ke kaiwa al’umma.

Har ya zuwa wannan lokaci, Kakakin rundunar ƴan sandan babban birnin tarayya Abuja, DSP Adeh Josephine, bai ce komai ba dangane da harin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci