OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

An Ceto Ɗan Shekara  Ɗaya Tare Da Mutane 11  A Zamfara

An Ceto Ɗan Shekara  Ɗaya Tare Da Mutane 11  A Zamfara

Photo Source: Blueprint

An kuɓutar da mutane 11 ciki har da wani yaro ɗan shekara daya daga hannun ƴan bindiga bayan wani gagarumin aikin ceto da aka yi a dajin Gando da ke karamar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara.

Rundunar ƴan sandan jihar ta bakin mai magana da yawunta, SP Mohammed Shehu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Ya ce a ranar Litinin, 17 ga Oktoba, 2022, wasu gungun ƴan bindiga sun kai farmaki ƙauyen Manye da ke karamar hukumar Anka.

Yayin da ƴan bindigan suka yi awon gaba da mata goma da wani yaro ɗan shekara ɗaya a dajin Gando da ke karamar hukumar Bukkuyum a jihar inda suka kwashe kwanaki uku a hannunsu. 

Ya kuma ce da samun rahoton kwamishinan ƴan sandan CP Kolo Yusuf ya tura ƙarin jami’an ƴan sanda na musamman domin karfafa wa ƴan banga a aikin ceton da suka yi.

Aikin wanda yayi sanadiyar samun nasara  tare da cikakken goyon bayan masu ruwa da tsaki musamman shugaban ƙaramar hukumar Anka.

Ya bayyana cewa an kai dukkan waɗanda aka ceto zuwa asibiti domin duba lafiyarsu, inda jami’an ƴan sanda suka bayyana su tare da miƙa iyalansu.

Kwamishinan ƴan sandan ya kuma yabawa shugaban karamar hukumar Anka bisa cikakken goyon baya da haɗin gwiwa a lokacin aikin ceto.

Ya kuma taya waɗanda abin ya shafa murnar samun ƴancinsu, ya kuma ba da tabbacin cewa, za a kama duk wadanda suka aikata wannan aika-aika a gurfanar da su a gaban kotu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci