OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Tinubu Ya Bayar Da Gudumawar Naira Miliyan 20 Ga Cocin Katolika A Otukpo

Tinubu Ya Bayar Da Gudumawar Naira Miliyan 20 Ga Cocin Katol

Bola Tinubu

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 20 ga cocin St. Francis Catholic Church Otukpo, a jihar Benuwe.

Rabaran Hyacinth Alia, ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar ne ya bayar da tallafin a wajen bikin cika shekaru ɗari na ɗarikar Katolika na Otukpo.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Isaac Uzaan, mai taimaka wa Alia kan harkokin yaɗa labarai ya fitar a Abuja.

Uzaan yace Cocin Cathedral na St. Francis Otukpo da Tinubu sun yi murna tare da limaman coci, da ɗaukacin ƴaƴan cocin kan wannan buki na farin ciki.

Ya ce cocin ta shafe shekaru 100 tana jajircewa wajen yaɗa bisharar ceto a Najeriya, musamman ga mutanen Benuwe ta Kudu.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC ya bayyana fatansa cewa idan aka yi addu’a da ayyuka masu kyau ƙasar za ta shawo kan ƙalubalen da ta ke fuskanta.

Hakazalika, ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnati, Sanata George Akume ya bayar da gudummawar Naira miliyan 10 ga cocin.

Akume wanda shi ne shugaban APC a Benuwe kuma tsohon gwamnan jihar ya samu wakilcin shugaban APC, Austin Agada.

Ya buƙaci al’ummar Binuwe da su dage da addu’a ga jihar da Najeriya domin shawo kan ƙalubalen da ake fuskanta.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci