OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Na Yafewa Osinbajo, Zan Yi Aiki Tare Da Kowa - Tinubu

Na Yafewa Osinbajo, Zan Yi Aiki Tare Da Kowa - Tinubu

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu ya ce ya yafewa mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo.

Tinubu ya bayyana haka ne a Kano, yayin da yake jawabi ga wasu ƙungiyoyi da suka goyi bayan Osinbajo a lokacin zaɓen fidda gwani na jam'iyyar.

A cewar Tinubu mutumin da ke neman gafara daga Allah, dole ne ya kasance a shirye ya gafarta wa wasu.

Tinubu ya ce ba shi da wani ƙulli a kan mataimakin shugaban ƙasa domin ya tabbatar da cewa zai yi aiki da kowa da kowa.

Ya bayyana cewa ya ziyarci Osinbajo a gidansa bayan kammala zaben fidda gwani, sannan kuma ya yi mu’amala da shi a lokuta da dama.

“Ba ni da komai a kansa, Na je gidansa bayan kammala firamare, kuma mun haɗu a wurare daban daban, cewar Jaridar Vanguard.

“Kuma wanda ya yi afuwa ga wanda ya nemi gafarar Allah, ya cancanci gafara,  Idan ba za ku iya yin gafara ba, yaya kuke roƙon Allah?  A waje na, komai ya wuce,” in ji shi.

In zaku iya tunawa Osinbajo na ɗaya daga cikin ƴan takarar shugaban ƙasa da suka fafata da Tinubu a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC.

Baya ga Osinbajo, wasu ƴan takarar shugaban ƙasa 13 sun haɗa da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, Gwamna Dave Umahi na Jihar Ebonyi da takwaransa na Jihar Kogi, Yahaya Bello.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci