OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Zan Rage Ƙarfin Iko Da Gwamnatin Tarayya Ke Da Shi - Tinubu

Zan Rage Ƙarfin Iko Da Gwamnatin Tarayya Ke Da Shi - Tinubu

APC Presidential Candidate, Bola Ahmed Tinubu

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu, ya bayyana ƙudurinsa na sake tsarin tarayyar Najeriya ta yadda ko wani yanki zai samu iko.

Tinubu yayi wannan bayani ne a yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓensa, kamar yadda Jaridar Allnews ta ruwaito a wanda shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar sa dake Abuja.

Shugaba Buhari ya yi alƙawarin kasancewa a sahun gaba wajen zaɓen tsohon gwamnan jihar Legas a matsayin wanda zai gaje shi.

Ya ce zaɓen Tinubu zai ƙara ƙarfafa nasarorin da gwamnatinsa ta samu domin ɗan takarar yana da ƙwarewa da hangen nesa.

 ”Zai zama matsala idan aka bar lamarin da zai haifar da koma baya ga ci gaban da ƙasarmu ta samu.  

"Bari in ƙara da cewa ina murna da karɓar muƙamin shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar APC.

“Ɗan takarar mu, Asiwaju Bola Tinubu ya yi fice sosai kan iya aiki, Ya tsaya tsayin daka a matsayinsa na mai bin tafarkin dimokaradiyya.

 Anashi jawabin, Asiwaju Bola Tinubu ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta sake duba tsarin dokokin ƙasar domin tabbatar da cewa an baiwa Jihohi karfin iko kan wasu muhimman batutuwa.

Ya ƙara da cewa, "Ya kamata a ware ƙarin kuɗaɗe ga Jihohi da Kananan Hukumomi ta yadda za su iya magance matsalolin cikin gida da kuma sauƙe nauyin da kundin tsarin mulki ya shimfida ga jama'a", in ji shi.

Tinubu ya kuma nuna damuwarsa kan yawan yaran da ba sa zuwa makaranta wanda a baya-bayan nan ya kai miliyan 20.

Yayin da ya bayyana cewa zai samar da wani aiki na musamman don magance matsalar, ruwaitowar Jaridar Vanguard.

“Bayar da fifiko ga matsalar ƙaruwar yaran da ba su zuwa makaranta a fadin kasar nan.

"Kawo ƙarshen wannan matsala zai baiwa dubun-dubatar yara damar samun ilimi, Hakan kuma zai rage adadin matasa masu zaman banza".

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci