OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

NELFUND ya gargadi dalibai suyi takatsantsan da shafukan intranet na jabu

NELFUND ya gargadi dalibai suyi takatsantsan da shafukan int

Asusun ba da lamuni na ilimi na Najeriya NELFUND, ya yi kira ga dalibai da su yi taka tsantsan tare da tabbatar da sahihancin duk wani shafin yanar gizo da ke ikirarin yana wakiltar asusun.

 

Wannan na zuwa ne a wata sanarwa da aka fitar a Abuja ranar Juma’a ta hannun shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na NELFUND, Nasir Ayitogo. 

 

“Hukumomin NELFUND sun fahimci wani talla na yaudara game da ‘Lamuncin Karatu na Tarayya’ da wasu yan damfara ke yadawa a shafin yanar gizon www.fedstudyloan-gov.ng suna basaja a matsayin sahihin shafin asusun dake rajistar tsarin rancen dalibai da ake sa ran Gwamnatin Tarayya ta yi. 

 

“NELFUND na son fayyace cewa ba ta da wata alaka da wannan shafin yanar gizon kuma ta yi kakkausar suka ga duk wani yunkuri na yaudarar daliban da ke neman taimakon kudin karatu.

 

NELFUND ta dauki tsaro da walwalar dalibanmu da muhimmanci kuma ta himmatu wajen samar da sahihin bayanai don ciyar da iliminsu gaba. ” in ji shi.

 

 A saboda haka, Ayitogo ya bukaci duk wanda wannan zamba ya shafa da ya gaggauta kai rahoto ga hukumomin da abin ya shafa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci