OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

LASEPA Ta Rufe Wasu Coci Da Otal Saboda Yawan Hayaniya

LASEPA Ta Rufe Wasu Coci Da Otal Saboda Yawan Hayaniya

Hukumar kare Muhalli ta Jihar Legas, LASEPA, ta rufe coci-coci, otal-otal, mashaya, da sauran cibiyoyi na wani dan lokaci a sassan jihar, sakamakon yawan hayaniya.

 

Tokunbo Wahab, Kwamishinan Ma'aikatar Muhalli da Ruwa na Jiha, ne ya wallafa hakan a shafinsa na X a ranar Juma'a. 

 

Yankunan da abin ya shafa sun hada da Ifako-Ijaiye, Abesan Estate, Abule-Egba, Alagbado, Command, da Dopemu.

 

Daga cikin wuraren da abin ya shafa akwai cocin Katolika, 1602 Hotel, Seventh Heaven Bar & Lounge, Lourita Hotel & Suites, God’s Porch Ministries, Wonderful Bible Prayer Ministries, White Pavilion Hotel, Quest Hotel & Suites, Excel Hotel & Suite, and HoneyComb Confectionery Ltd

 

Sanarwar ta ce an rufe cibiyoyin na wani dan lokaci don "tilasta bin ka'idojin muhalli. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci