OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Yan ta'adda sun kashe wani kwamandan soji a Katsina

Yan ta'adda sun kashe wani kwamandan soji a Katsina

Yan ta'adda sun kashe kwamandan wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a jihar Katsina a wani harin kwantan bauna da aka kai musu. 

 

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, wata majiya ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, inda aka ajiye marigayin mai mukamin Manjo a rundunar soji a wani asibiti dake Katsina.

 

An yiwa kwamandan wanda aka boye sunan sa kwanton bauna ne a kauyen Malali da ke karamar hukumar Kankara a lokacin da yake amsa kiran kai dauki wajen dakile harin da yan ta'addar suka kaiwa abokan aikin sa.

 

Majiyoyi sun bayyana cewa ‘yan bindiga sun mamaye yankin, kuma duk da martanin da kwamandan ya yi ta hanyar amfani da motar Hilux maimakon motar Amoured Personnel Carrier (APC), wasu mahara sun bindige shi sannan suka harbe shi a kai.

 

Wani mazaunin kauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa an yi musayar wuta tsakanin ‘yan bindiga da jami’an soji inda jami’in sojin daya je ya dauko gawar shi ma ya samu rauni.”

 

 Jami’an tsaron sunyi ta harbin iska a inda suke tunanin maboyar yan bindigar take ba tare da sunyi martani ba saida suka bari kwamandan ya iso sannan suka fara harbin sojojin" Majiyar ta kara da cewa

 

 A baya-bayan nan ne aka fuskanci munanan hare-hare a kauyukan yankin inda Al'ummar yankin suka fara hijira suna barin wajen.

 

Har yanzu jami’in hulda da jama’a na Brigade 17 a Katsina, Oiza Ehinlaidlye, bai amsa tambayoyi ba, kamar yadda rahoton ya bayyana.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci