OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yawan Talla Na Hana Wasu Yara Mata Zuwa Makaranta A Kano— Ma'aikatar Ilimi

Yawan Talla Na Hana Wasu Yara Mata Zuwa Makaranta A Kano—

Tallace tallacen da yara mata ke yi a Kano na daga abinda ke hana su zuwa makaranta.

Shugabar sashen kula da ilimin yara mata ta ma'aikatar ilimi a Kano, Hajiya Amina Kassim ce ta bayyana haka , yayin da ake bikin yara mata ta duniya.

Sha daya ga watan Oktoban kowace shekara ne ake bikin yara mata ta duniya, wanda majalisar dinkin duniya ta ware don waiwaye kan halin da yara mata suke ciki.

A sassan duniya daban daban, ilimi, tsaro da lafiyar yara mata na daga bangaren da suka fi bukatar kulawa.

Shugabar sashen kula da ilimin yara mata, Amina Kassim ta ce talla na daga kalubalen da ke hana yaran samun ilimin muhammadiyya da na boko.

Tace duk da a halin da ake ciki ba za’a iya hana yaran talla baki daya ba, amma akwai hanyoyin da ake kokarin bi wajen ganin hakan bai hana su samun ilimi ko sanaar dogaro da kai ba.
Amina Kassim tace zuwa yanzu, sun fara shiga kananan hukumomin dake Kano, inda shugabannin kasa, wato masu rike da sarautun gargajiya ke zakulo kalubalen da yaran su mata ke fuskanta, tare da bayar da hadin kai wajen magance su.
Shugabar sashen kula da ilimin yara matan, tace ana sa ran kafin karshen shekarar nan, a samu gagarumin ci gaba wajen karuwar yara a makarantu, da ma kiyaye lafiyar su da rayukan su.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci