OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

An fallasa wani malamin jami'ar Nsukka da yayi kokarin lalata da matar aure

An fallasa wani malamin jami'ar Nsukka da yayi kokarin lalat

An kama wani malami a Jami’ar Najeriya Nsukka UNN a cikin ofishinsa yana kokarin haikewa wata dalibarsa.

 

 Kamar yadda shafin UNNGram ya wallafa a shafin Instagram, mutumin da ba a bayyana sunansa ba, wanda aka ce malami ne a Makarantar Koyon Ilimi ta Jami’ar, an dade ana zargin sa da yin lalata da dalibai mata hakan yasa sauran daliban suka dana masa tarko.

 

 A cikin wani faifan bidiyo na lamarin da aka yada a kafar X, an ji wata murya tana cewa an dade ana bin malamin an kuma tattara dukkan sakonnin da bayanan muryar da ya aika wa wata daliba da matar aure ce.

 

An jiyo muryar dake daukar bediyon na cewa "Mun yi ta bibiyar lamarin tun daga ranar daya fara bibiyar matar auren kamar yadda kuke gani, muna da duk taɗi, bayanin murya, bidiyo da komai ”

 

Mai bediyon ya cigaba da bayanin mijin dalibar ne ya shirya wa malamin tarko da tallafin wasu daliba domin malamin ya dade yana bibiyar dalibar taki bashi hadin kai.

 

Dalibar tayi kokarin bawa malamin kudi domin ya kyale ta amman yaki yarda hakan yasa suka zabi su hada mishi tarko su fallasa abubuwan dayake yi a idon duniya.

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci