OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

‘Yan Sanda Sun Tabbatar Da Damke Dan Bindiga, Da Kwato Bindigu Biyu A Kaduna

‘Yan Sanda Sun Tabbatar Da Damke Dan Bindiga, Da Kwato Bin

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da cafke wani dan bindiga tare da kwato bindigu kirar AK-47 da AK-49 cike da alburusai a jihar.

Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin mai magana da yawun rundunar, Mohammed Jalige a yau (Asabar).

A cewar sanarwar, biyo bayan wani sahihin rahoton sirri, jami’an rundunar sun tarwatsa sansanin masu garkuwa da mutane a dajin Galadimawa na karamar hukumar Giwa a jihar.

Jalige ya bayyana cewa, bayan wani kazamin fada da ‘yan sandan suka yi da su, 'yan ta'addan sun diba na kare.

Ya kara da cewa harin ya sa ‘yan bindiga da dama sun tsere da raunukan harbin bindiga.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito, Jalige ya ce: “Duk da haka, jajirtattun ‘yan sandan sun yi nasarar cafke daya daga cikin ‘yan bindigan dauke da bindigu kirar AK 47/49 da harsashi guda biyar masu girman gaske 7.62 X 39mm.

“Sauran abubuwan da aka kwato sun hada da wayoyin hannu na Tecno guda uku da fitilar wuta.

“A halin yanzu wanda ake zargin yana hannu ana gudanar da cikakken bincike kuma har yanzu jami’an na ci gaba da kokarin kamo sauran abokan na sa”.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna, Yekini Ayoku ya yaba wa ‘yan sandan bisa hobbasa da suka yi wanda ya kawo nasarar hakan.

Kwamishinan ya kuma yi alkawarin ci gaba da zage damtse wajen yaki da masu aikata laifuka tare da jaddada aniyar sa na hada kai da sauran hukumomin tsaro a jihar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci