OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

'Yan Jam'iyyar APC 1,868 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Sokoto

'Yan Jam'iyyar APC 1,868 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Sokoto

APC

Akalla 'yan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki 1,868 ne suka fice daga jam’iyyar zuwa PDP a jihar Sokoto.

Kakakin jam’iyyar PDP, Malam Hassan Sanyinnawal ne ya bayyana hakan a Sokoto a yau (Alhamis).

Sanyinnawal ya ce wadanda suka sauya sheka sun samu tarbar shugaban jam’iyyar PDP, Alhaji Bello Goronyo ranar Laraba a jihar.

Ya kuma yi bayanin cewa, ‘yan kasuwa ne daga yankuna 10 da ke fadin jihar.

Shugaban wanda ya samu wakilcin shugaban jam’iyyar na shiyyar Sakkwato ta tsakiya, Muhammad Dangoggo ya bada tabbacin cewa za a yi adalci tsakanin su da tsofaffin ‘ya’yan jam’iyyar.

A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya kuma yi kira da a ba su goyon baya domin samun nasara a zaben 2023 mai zuwa.

Da yake magana a madadin wadanda suka sauya shekam, Lawali Lalala ya yi alkawarin goyon bayan su ga jam’iyyar PDP, inda ya kara da cewa sun yanke shawarar ne bisa nasarorin da gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal ta samu.

Da yake karbar su cikin jam’iyyar, dan takarar gwamna a jam’iyyar, Sa’idu Umar, ya yi alkawarin yin aiki tare da wadanda suka sauya shekan domin samun nasarar jam’iyyar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci