OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yan Bindiga Sun Kashe Direba, Sun Sace Fasinjoji Uku A Katsina

Yan Bindiga Sun Kashe Direba, Sun Sace Fasinjoji Uku A Katsi

Bandits

Wasu ‘yan bindiga da ke aika-aika a hanyar Magamar Jibia a jihar Katsina sun kashe wani direban mota yayin da suka yi awon gaba da fasinjoji uku.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da hakan.

Isah ya ce mai yiwuwa 'yan fashin sun tafi ne da fasinjojin da ba a bayyana adadin su ba a yayin harin.

A cewar sa: “’Yan ta’addan sun tare motoci biyu a kan hanyar Magamar zuwa Jibia inda suka harbe daya daga cikin direbobin.

“Ba su shiga garin ba. An fatattaki ‘yan ta’addan.

“Daga baya an tsinci gawa a wani daji dake kusa.

"Wasu fasinjojin da ke cikin motocin biyu ma ba a gan su ba, kuma ana kyautata zaton 'yan ta'addan ne suka tafi da su."

Majiyoyi sun ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 9:15 na dare.

A yayin da al’ummar yankin suka samu kwanciyar hankali a ranar Lahadi, wasu mazauna garin sun yi zargin cewa ‘yan bindigan sun kashe mutane biyu a yayin harin kafin a fatattake su.

Haka kuma majiyoyin sun kara da cewa tun bayan faruwar harin an baza jami'an tsaro a cikin garin suna sintiri.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci