OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3, Sun Kuma Yi Garkuwa Da Wasu A Imo

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3, Sun Kuma Yi Garkuwa Da Wa

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe wani makanikin mota a mahadar kasuwar Nkwo Orji da ke kan titin Owerri-Okigwe, a jihar Imo.

An kashe Valentine Enwerem ne a yammacin ranar Juma’a, kuma bayan harbe shi har lahira, ‘yan bindigar sun kuma yi garkuwa da mutane ukun da yake dauke da su a cikin wata mota.

Lamarin dai ya haifar da firgici a yankin yayin da ‘yan bindigan suka ci gaba da harbe-harbe a lokacin da suke hanyar ficewa daga wurin.

Abokan aikin marigayin sun shaida wa wakilin jaridar Punch a shagon ​shi​ a ranar Asabar, inda suka ce wadanda suka kashe shi sun nufi karshen hanyar Okigwe bayan sun kashe shi tare da yi awon gaba da mutanen motarsa.

“Sun ce ba shi suka zo nema ba amma sun nemi ya ba su hadin kai. 

"Daga baya sun harbe shi har lahira sannan suka zagaya zuwa karshen hanyar Okigwe bayan sun yi garkuwa da mutanen da ke cikin motar," kamar yadda wani abokin aikinsa ya bayyana.

“Ya fito daga karamar hukumar Ikeduru ta jihar Imo kuma matarsa ​​tana sayar da kayayyaki kusada shagonshi.

 "Wannan babban abin takaici ne.

"Mun ji zafi kuma mun ji haushin rashin sa."

 A halin da ake ciki kuma, a yammacin ranar Juma’a ne aka yi garkuwa da wasu jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a wasu wurare biyu a karamar hukumar Isiala Mbano ta jihar.

Wadanda aka kashe din dai su ne Cif Godson Obijiaku da aka yi garkuwa da shi a unguwarsu da ke Amauzairi, sai kuma wani dan siyasa daga karamar hukumar Ikeduru da aka fi sani da ‘Ability’, an yi garkuwa da shi a wani kantin magani da ke Amaraku.

Lamarin dai ya haifar da firgici a yankunan yayin da jama'a suka yi ta gudu a cikin gidajensu tare da rufe harkokin su.

Wata majiya da ba ta so a ambaci sunanta ta ce, “An yi garkuwa da Cif Obijiaku, mai neman takarar shugabancin karamar hukumar a zabe mai zuwa.

“Lokacin da suke zuwa Amaraku, sai suka ga wata mota kirar Tundra a ajiye a gaban wani shagon sayar da magunguna, sai suka tsaya, suka je can suka yi garkuwa da Chief Ability sannan suka saki harbe-harbe da dama a lokacin da suke hanyar fita daga muhallin.

 "Yankin yana cikin firgita, ya kamata gwamnati ta yi wani abu."

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Micheal Abattam, har yanzu bai amsa kira da sakonnin da aka aika masa ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci