OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Katsina Ta Baiwa Ma’aikatar Lafiya Ta Tarayya Tallafin Fili Mai Fadin Hekta 50

Katsina Ta Baiwa Ma’aikatar Lafiya Ta Tarayya Tallafin Fil

Gwamnatin jihar Katsina ta baiwa ma’aikatar lafiya ta tarayya gudummawar fili mai fadin hekta 50 don taimakawa wajen cimma wannan burin mayar da babban asibitin Daura zuwa cibiyar kula da lafiya na tarayya.

 Sakataren gwamnatin jihar Alhaji Muntari Lawal ne ya bayyana hakan a ofishin sa a lokacin da mambobin kwamitin tantance mayar da babban asibitin Daura zuwa cibiyar kiwon lafiya ta tarayya suka ziyarci ofishin sa.

 Kwamitin daga ma’aikatar lafiya ta tarayya ya samu jagorancin Alhaji Hassan Sallau, Dokta Sunday Atinku, wanda ya wakilci karamin minista, Dokta Gilabert Shetak, wanda ya wakilci darakta mai kula da albarkatun jama’a da kuma Misis Bilkisu Abdullahi, daga ofishin babban sakatare.

 Idan za'a iya tunawa Gwamnatin Tarayya ta amince da mayar da Babban Asibitin Daura zuwa Cibiyar Kiwon Lafiyar Jama’a bayan da aka mayar da Cibiyar Kiwon Lafiya ta Katsina zuwa Asibitin Koyarwa.

 A cewar SSGn Katsina, an umurci ma’aikatar lafiya ta jihar da ta tuntubi ma’aikatar filaye da safiyo don fara aikin shata gonakin da ke Daura cikin gaggawa tare da saukaka bayar da takardar shaidar zama ga ma’aikatar lafiya ta Tarayya.

 Muntari Lawal ya bada tabbacin jajircewar Gwamnati wajen ganin an samu nasarar samar da sabuwar cibiyar kula da lafiya ta tarayyan domin cigaban al'ummar jihar baki daya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci